A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, a ranar Talata, 25 ga watan Agusta 2026, wanda ya yi daidai da 12 ga Rabi’ul Awwal 1448 bayan Hijira, an gudanar da zagayen murnar Mauludin Manzon Allah (S.A.W.A) a wurare daban-daban na ƙasar Najeriya.
Wannan biki da ake gudanarwa duk shekara a garuruwa daban-daban na Najeriya, ya samu halartar dimbin al’umma daga sassa daban-daban, ciki har da maza da mata, yara da matasa, da kuma tsofaffi. Mahalarta sun fito sanye da sababbin fararen kaya, tare da sanya turare, yayin da suke tafiya cikin jerin gwanon cikin tsari.
Daga cikin masoya Manzon Allah (S.A.W.A) da suka halarci wannan zagaye akwai mabiyan Harkar Musulunci ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H). Mabiyan Harkar sun halarci taron cikin tsari da haɗin kai, ɗauke da tutoci da hotunan wasu daga cikin jagororin gwagwarmaya, ciki har da Imam Khumaini (Q), Shahidin Jagora (Q), Shahid Sayyid Hassan Nasrullah, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Mujtaba Khamene’i, Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) da sauran fitattun jagororin gwagwarmaya.
A yayin zagayen, mahalarta sun ci gaba da bayyana ƙauna da girmamawa ga Manzon Allah (S.A.W.A) da iyalansa tsarkaka, inda suka rera waƙoƙi da yabon Manzon Allah (S.A.W.A) da Ahlul Baiti (A.S).
Haka kuma, a yayin gudanar da wannan biki, an raba alawoyi, biskit da dafaffen abinci ga jama’a da masu kallo, lamarin da ya ƙara sanya yanayin garuruwan ya kasance cikin farin ciki da murnar zagayowar haihuwar Manzon Allah (S.A.W.A).
Ya kamata a lura cewa wannan shi ne zagayen farko na bukukuwan Mauludin Manzon Allah (S.A.W.A) da aka gudanar a Najeriya, yayin da ake sa ran sake gudanar da wani zagaye a ranar 17 ga watan Rabi’ul Awwal a sassa daban-daban na ƙasar.



















Ra'ayinka